Ƙwannafi (acidity) shi ne sunan da aka saba amfani da shi na alamomin da acid na ciki ke kawowa idan ya ɓata hanyar abinci (esophagus) ko bangon ciki:
- Dawowar acid (acid reflux): acid yana hawa daga ciki zuwa maƙogwaro.
- Zafin ƙirji (heartburn): zafin da dawowar acid ke kawowa a ƙirji.
- GERD (GORD): gastro-oesophageal reflux disease, sunan da likitoci ke amfani da shi idan dawowar acid tana ta faruwa.
- Rashin narkewar abinci (indigestion, dyspepsia): rashin jin daɗi, jin ciki ya cika da gyatsa bayan cin abinci, sau da yawa daga acid ɗin nan.
Yawancin mutane suna samun ƙwannafi ko rashin narkewar abinci lokaci zuwa lokaci, kuma yawanci ba alamar wani abu mai tsanani ba ne.

